Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 40 A Kebbi Da Zamfara

Akalla mutane 40 ne ‘yan bindiga su ka hallaka, ciki kuwa har
da jami’an tsaro a jihohin Kebbi da Zamfara a ranar Lahadin
da ta gabata.

Daga cikin mutanen da aka kashe akwai ‘yan sandan kwantar da tarzoma guda shida, da fararen hula 36 a kauyen Dan Umaru da ke Karamar Hukumar Zuru ta Jihar Kebbi.

Mazauna yankin sun shaida wa manema labarai cewa, an gudanar da jana’izar mutane 27, wasu mutane da dama kuma sun samu raunuka sakamakon harin.

Sun sun ce maharan sun kuma sace mutane da daruruwan dabbobi a kauyukan da ke makwaftaka da su.

Exit mobile version