Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Ta’addanci: ‘ Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 17 Sun Kuma Hana Jana’izar Su A Zamfara

Wasu ‘yan bindiga sun hallaka akalla mutane 17, a wani mummunan hari da su ka kai kauyuka uku da ke karamar hukumar Birnin Magaji ta jihar Zamfara.

Mazauna yankunan sun bayyana cewa, ‘yan bindigar sun shiga kauyukan ne a kan babura ranar Asabar da ta gabata, inda su ka kai hari kauyen Gidan Kaso su ka kashe akalla mutane 7, sannan su ka hana gudanar da jana’izar matattun.

Wani mazaunin garin Tukur Yusuf, ya ce ‘yan bindigar sun hana jama’a gudanar da Sallar Jana’izar matattun har sai lokacin da jami’an tsaro suka kai agaji.

Haka kuma, ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyen Dambo a ranar Lahadin da ta gabata, inda su ka hallaka mutane 4 tare da kwashe masu awaki. Wata majiya ta ce, mutane bakwai daga kauyen Kokeya da su ka kai agaji kauyen Dambo sun gamu da ajalin su a hannun ‘yan bindigar, yayin da su ka yi kokarin taimaka wa wadanda harin ya shafa a garin Dan Dambo.

Exit mobile version