Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

‘Yan Bindiga Sun Kai Wa Tawagar Tsohon Gwamnan Jihar Imo Hari

‘Yan bindiga sun kai hari a kan tawagar tsohon gwamnan jihar Imo Ikedi Ohakim tare da kashe jami’an ‘yan sanda huɗu.

‘Yan bindiga sun kai hari a kan tawagar tsohon gwamnan jihar Imo Ikedi Ohakim tare da kashe jami’an ‘yan sanda huɗu.

Lamarin ya faru ne a garin Oriagu da ke ƙaramar hukumar Ehime Mbano ta jihar, lokacin da tsohon gwamnan ke kan hanyar sa ta dawowa daga wata ziyara da ya kai tare da ‘ya’yan sa biyu.

Ikedi Ohakim dai ya tsallake rijiya-da baya yayin harin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yan sanda huɗu da ke cikin tawagar sa.

‘Yan bindigar sun lalata ɗaya daga cikin motocin tawagar tsohon gwamnan, bayan sun kasa samun dama a kan tsohon gwamnan ba kamar yadda rahotonni su ka bayyana.

Ikedi Ohakim ya taba riƙe muƙamin gwamnan jihar Imo daga shekara ta 2007 zuwa 2011.

Exit mobile version