Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

’Yan Bindiga Sun Budewa Masallata Wuta A Jihar Neja

Akalla Mutum 15 ne suka rasu bayan ’yan bindiga suka bude wuta a lokacin da suke Sallar Asuba a wani masallaci dake kauyen Ba’are a Karamar Hukumar Mashegu ta Jihar Neja.

Rahotanni sunce maharan sun kuma jikkata mutane da dama, inda aka garzaya da su zuwa Babban Asibitin Kontagora domin kulawa da su.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Neja, Monday Bala Kuryas, ya tabbatar da harin, amma ya ce, “Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja ta tura jami’an tsaro somin kare rayuka da dukiyoyi Al’ummar yankin.

A cewarsa, mutum tara ne aka kashe a harin, sabanin adadin da jama’ar garin suka bayyana.

Kwamishinan ’Yan Sandan ya kuma ba wa jama’a tabbacin samun cikakkiyar kariya daga jami’an tsaro, yana mai rokon su da su rika taimakawa da bayanan sirri.

Kimanin wata biyu ke nan da wasu mahara suka hallaka mutum 18 a lokacin da suke Sallar Asubahi a wani masallaci a kauyen Mazakuka a Karamar Hukumar ta Mashegu.

Exit mobile version