Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Yaki Da Ta’addanci: Za A Aika Da Karin Jiragen Yaki Zamfara Da Katsina

Rundunar Sojin saman Najeriya ta na shirye-shiryen aikewa da karin jirage masu saukar ungulu na yaki kirar Agusta 109 zuwa jihohin Zamfara da Katsina domin fatattakar ‘yan bindiga.
Rundunar za ta aike da jiragen ne bayan bikin cika shekaru 55 da kafuwar rundunar sojin saman da zai gudana a ranar litinin mai zuwa, a matsayin wani sabon yunkuri domin kammala murkushe ‘yan bindigar da ke haifar da barazanar tsaro a jihohin biyu.
Kakakin rundunar sojin saman Najeriyar Air Commodore Ibikunle Daramola, ya tabbatar da cewa baya ga jiragen akwai kuma tarin dakaru da za a sake aikewa jihohin domin kawo karshen hare-haren ‘yan bindigar.
Haka zalika ya ce za a bude wata shalkwata ta musamman a birnin Gwari da za ta rika kula da dakaru da kuma jiragen da ke yaki a jihohin Kaduna da Katsina masu fama da hare-haren ‘yan bindiga da ayyukan masu garkuwa da mutane.
Hare-haren ‘yan bindiga da garkuwa da mutane da satar shanu da kuma rikicin kabilanci dai na ci gaba da ta’azzara a jihohin Katsina Zamfara da jihar Kaduna, inda a kowacce rana jama’a kan rasa rayukan su.

Exit mobile version