Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Yaki Da Ta’Addanci: Sojojin Najeriya ‘Sun Kashe ‘Yan Bindiiga Fiye Da 50 A Jihar Kaduna

Rahotanni daga Najeriya sun nuna cewa rundunar sojin sama ta kasar na samun nasara a hare-hare ta sama da take kai wa sansanonin ‘yan fashin daji da ke PR NIGERIA, Jihar Zamfara da kuma Kaduna.

Kafar watsa labarai ta PR Nigeria ta ruwaito cewa jiragen saman sojojin kasar sun kai hari a sansonin yan fashin dajin da ke dajin Kawara a karamar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna.

Wata majiyar tsaro ta ce ‘yan fashin daji kusan hamsi ne suka hallaka a hare-haren ta sama a karshen mako

Majiyar ta kuma ce wani jirgin sama mai saukar ungulu na rundunar sojin sama ya gano wani gungun yan fashin daji sanye da bakaken tufafi, tare da shanu da suka sace kusa da kauyen Kawara a karamar hukumar Giwa.

“Lokacin da suka hango jirgin saman, yan bindigar sun tsere sun buya tsakanin shanu”, in ji majiyar.

Jiragen saman Najeriya sun yi luguden wuta a sansanonin ‘yan fashin daji a Zamfara

Majiyar ta kuma ce bayan da yan bindigar suka taru a wani wurin tsallaka ruwa, jirgin saman ya rika yi musu luguden wuta.

“Wasu daga cikin wadanda suka rasa rayukansu sun rika kokarin tserewa lokacin da jirgin saman ya yi mu su luguden wuta”, a cewar PRNigeria.

Mahukuntan Najeriya sun kara kaimi a kwanakin baya baya nan a matakan da suke dauka domin magance matsalar yan fashin daji.

Baya ga hare-hare ta sama, mahukunta a Najeriya sun kuma dauki matakan dakatar da layukan sadarwa a jihar ta Zamfara.

Sai dai masana sun ce idan ana son matakin ya yi, akwai bukatar ganin cewa mahukuntan Najeriyar sun hada karfi da karfe da kasashe makwabta.

Exit mobile version