Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Samar Da Tsaro: Nijeriya Za Ta Aike Da Karin Jiragen Yaki Zamfara Da Katsina

Rundunar Sojin saman Nijeriya ta na shirin aikewa da karin jiragen yaki kirar Agusta 109 zuwa jihohin Zamfara da Katsina da ke fuskantar matsalar hare-haren ‘yan bindiga.

Wata majiya ta ce, rundunar sojin za ta aike da jiragen ne bayan bikin cika shekaru 55 da kafuwar rundunar sojin sama da zai gudana a ranar Litinin mai zuwa, a matsayin wani sabon yunkuri domin kammala murkushe ‘yan bindigar da ke haifar da barazanar tsaro a jihohin uku.

Kakakin rundunar sojin saman Nijeriyar Air Commodore Ibikunle Daramola ya tabbatar da cewa, baya ga jiragen akwai kuma tarin dakaru da za a sake aikewa jihohin domin kawo karshen hare-haren ‘yan bindigar.

Ya ce za a kuma bude wata helkwatar musamman a Birnin Gwari da za ta rika kula da dakaru da kuma jiragen da ke yaki a jihohin ciki har da Kaduna. Kakakin ya ce, Babban Hafsan sojin saman Nijeriya Air Marshal Sadique Abubakar, tare da Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ne za su kaddamar da helkwatar.

Exit mobile version