Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Yaki Da Ta’addanci : Shugabannin Ecowas Sun Ware Dala Miliyan Dubu Daya

Shugabannin kasashen Yammancin Afirka sun amince da wani shirin yaki da ayyukan ta’addanci da za a kashe dalar Amurka miliyan dubu daya tsakani 2020 zuwa 2024 a yankin.

Shugaban kungiyar Ecowas ko kuma Cedeao kan kuma shugaban  kasar Nijar Mahamadou, Issoufou ne ya sanar da haka a karshen taron da ya samu halartar shugabannin yankin na yammacin Afirka a birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso.

Har ila yau kasashen Mauritaniya da Kamaru da kuma Chadi, wadanda ba mambobi ba ne a kungiyar sun halarci wannan taro tare da daukar alkawarin bayar da ta su gudunmuwa.

Shugabannin na Ecowas sun ce za a yi amfani da wadannan kudade ne domin karfafa rundunonin kasashen da kuma rundunar G5-Sahel, kuma a lokacin taron kungiyar ta Ecowas da za a yi cikin watan Disamba mai zuwa ne, za a fayyace yadda shirin zai gudana.

Kafin wannan yunkuri na kungiyar Ecowas, tu ni kasashen biyar na yankin Sahel wato Burkina Faso, Chadi, Mali, Mauritania da kuma Nijar suka sanar da kafa runduna ta musamman wato G5-Sahel domin fada da ayyukan ta’addanci a yankunsu.

Exit mobile version