Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Rikicin Mali: Shugabannnin ECOWAS Za Su Sake Tattaunawa

Shugabannin kasashen kungiyar yammacin Afirka wato Ecowas za su gudanar da taro na musamman a yau Litinin domin bayar da shawara kan matakan da za a dauka don kawo karshen rikicin Mali.

Taron wanda za su gudanar ta intanet na zuwa ne bayan ziyara sau biyu da wakilai da kuma shugabannin suka kai a Bamako, babban birnin kasar wadda ta gaza shawo kan rikicin da ke faruwa tsakanin Shugaba Ibrahim Boubacar Keita, da ‘yan hamayya da ke son ya sauka daga mulki.

Shugaban kungiyar ta Ecowas, wanda shi ne shugaban Jamhuriyar Nijar, Muhammadou Issoufou, a ranar juma’a ya ce zai dauki tsauraran matakai domin shawo kan rikicin kasar.

Gamayyar jam’iyyun adawa, wadda ake kira M5-RFP, ta yi watsi da kira-kirayen kafa gwamnatin hadin kan kasa, inda ta dage cewa dole shugaba Keita, ya sauka daga mulki sannan a kafa gwamnatin rikon kwarya.

Sai dai su shugabannin Ecowas sun doge ne cewa dole a bi kundin tsarin mulki wurin kawo sauyi a kasar ta Mali.

Exit mobile version