Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Yajin Aiki: Buhari Ya Umurci Ministan Ilimi Ya Sulhunta Da ASUU Nan Da Mako Biyu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu ya kawo ƙarshen yajin aikin malaman jami’o’in cikin makonni biyu masu zuwa.


Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Talatar nan inda ya bayar da umarni ga ministan da ya sasanta abubuwan da ake taƙaddama a kai ya kuma kai masa rahoto.


A ranar Talatar nan ne Shugaba Buhari ya tattauna da ma’aikatu da masu ruwa da tsaki a ɓangaren Ilimi da za su iya warware wannan tirka-tirkar.


Shugaban ya kira su ne domin ya samu ƙarin bayani kan dalilin da ya sa wannan yajin aikin ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.


To sai dai wasu majiyoyi sunce Shugaban Ya umarci Ministan ya gayyaci ASUU domin sasantawa da ita da sauran kungiyoyin jami’o’i da ke yajin aiki.

Exit mobile version