Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Yadda Aka Gudanar Da Addu’o’In Tunawa Da ‘Yar’Adua Bayan Cika Shekara 13 Da Rasuwa

Gamayyar ƙungiyoyin magoya bayan jam’iyyar PDP, sun
shirya taron addu’’o’i da karatun Al’Qur’ani mai girma domin
tunawa da tsohon Shugaban Ƙasa marigayi Umaru Musa
‘Yar’adua a masallacin helkwatar jam’iyyar da ke Katsina.

Taron addu’o’in dai ya na zuwa ne, bayan marigayi ‘Yar’adua cya cika shekaru 13 da rasuwa a ranar Juma’ar da ta gabata.

Da ya ke jawabi a wajen taron, Shugaban kwamitin riƙon ƙwarya na jam’iyyar PDP da ya samu wakilcin Lawal Rufa’i Safana, ya ce shirya taron addu’o’in ya zama wajibi, duba da gagarumin ci-gaban da marigayin ya kawo wa Nijeriya lokacin da ya ke mulki.

Ya ce ‘yan Nijeriya ba za su taɓa mantawa da ‘Yar’adua ba, saboda gudummawar da ya ba kasar nan a tsawon rayuwar sa.

Mai riƙon muƙamin Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar PDP Hamza Yunusa Jibiya, ya bayyana marigayi ‘Yar’adua a matsayin uba, wanda ya kamata a yi koyi da shi kuma shugaba mai gaskiya da hangen nesa.

Exit mobile version