Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Dattawan PDP Sun Ce Ba Su Yarda Da Tsaida Dan Takara 1 Daga Arewa Ba

Dattawan jam’iyyar PDP na arewacin Nijeriya sun yi taron gaugawa a Abuja, inda su ka nuna rashin amincewa da duk wani taro da ke nuna fitar da dan takara daya daga arewa gabanin zaben fidda gwani.

Taron, wanda ya hada tsofaffin gwamnonin jam’iyyar PDP, ya
gudana ne a karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Jigawa
Sule Lamido da tsohon minista Adamu Maina Waziri.

Matsayar dattawan na jam’iyyar PDP, ta nuna duk wani taron
takaita ‘yan takara irin wanda aka bukaci Janar Ibrahim
Babangida ya jagoranta, da barin wasu a gefe alhali su na da
muradin gwada farin jinin su ba daidai ba ne.

Sule Lamido, ya ce rudanin ya shafi yadda shugaban kungiyar
dattawan arewa Farfesa Ango Abdullahi ya fitar da sanarwa,
bayan wani taro da ya nuna an zabi mutane biyu daga cikin ‘yan
takarar domin wakiltar arewa, wadanda su ka hada da gwamna
Bala Muhammad na jihar Bauchi da Sanata Bukola Saraki.

Za a dai gudanar da taron zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP
ne a ranakun 28 da 29 ga Mayu na shekara ta 2022.

Exit mobile version