Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Yabo: Ministan Yada Labarai Ya Ce Matakan Tinubu Na Gyara Kura-Kuran Baya Ne

Mohammed Idris

Mohammed Idris

Gwamnatin tarayya ta ce shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ɗauki wasu matakai da tsare-tsare ne domin gyara wasu kura-kuran da aka tafka a baya domin dawo da tattalin arzikin Najeriya da ƙarfin  sa.

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan al’umma Mohammed Idris ne ya bayyana haka a nan Abuja a wata ganawa da ya yi da ƴan jarida domin bayyana yadda ƙasa za ta yi bikin cika shekara 64 da samun ƴancin kai.

Ya ce mulkin shugaba Tinubu, ya kawo wasu muhimman tsare-tsare domin gyara kura-kuran da aka yi a baya, tare da dawo da martabar Najeriya musamman a ɓangaren tattalin arziki.

Ministan yada labaran ya ce duk da matsalolin da aka samu da wahalhalun da ƴan ƙasa suka shiga sanadiyar matakan,

shugaba Tinubu na cigaba da ƙoƙarin inganta tattalin arzikin ƙasa da sanya ta a hanya mai ɗorewa da kowa zai ji daɗi.

Muhammad Idris, ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin manyan matsalolin da suka hana ƙasa cigaba shi ne hana ƙananan hukumomi sakat,

Amma shugaban ƙasa ya ba su ƴanci domin kai romon dimokuraɗiyya kowane lungu da saƙo.

Exit mobile version