Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

APC Ta Ce Gwamnatin Tinubu Ba Za Ta Sauya Matakan Ta Ba

APC (1)

APC (1)

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta shaida wa ƴan adawa cewa, su daina tunanin gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu za ta sauya matsayin ta dangane da matakan da take ɗauka a ƙasa.

Jam’iyyar ta kuma yi watsi da iƙirarin ƴan adawa na tafka maguɗi a zaɓen gwamnan jihar Edo da ya gudana a ranar 21 ga watan Satumban da ya gabata.

A ranar Alhamis ɗin nan ne, Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar adawa ta PDP ta yi zargin cewa, APC ta tafka maguɗi a zaɓen Edo domin cimma wata manufa ta mayar da Najeriya kan tsarin jam’iyya guda da ke mulkin har abada a kasa.

A yayin gabatar da jawabi ga manema labarai a birnin Abuja, Sanata Adophus Wabara ya bayyana damuwar sa kan halin da Najeriya ke ciki na taɓarɓarewar tattalin arziki, matsalar da ya ce, tsare-tsaren gwamnatin APC ne suka haddasa.

Sai dai a yayin mayar da martani a yau Juma’a, Darektan Yaɗa Labarai na APC, Alhaji Bala Ibrahim, ya shaida cewa, ko koɗan jam’iyyar ta APC bata da aniyar wargaza dimokurɗiyyar Najeriya.

Da dama daga cikin ƴan Najeriya na ci gaba da kokawa kan matakan gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu da suka ce sun jefa su cikin ƙuncin rayuwa, inda a baya-bayan aka ƙara samun tashin farashin litar man fetur a daidai lokacin da takawa ke kokowa kan tsadar rayuwa.

Exit mobile version