matasa a duniya na murnar ranar matasa masu sana’a ta duniya da aka yi wa take da ‘WORLD YOUTH SKILL DAY’ a Jihar Kano, ma ba a bar su a baya ba.
Matasan sun fito domin nuna baiwar su da ƙwarewar su a fannin ƙirƙirar na’urorin zamani da sarrafa kayayyaki na cikin gida domin amfanin al’umma.
Aƙalla matasa 136 ne, suka baje-kolin fikirar su a fannin ƙirƙire-ƙirƙiren na’urori daban-daban masu amfani ga rayuwar al’umma a Jihar Kanon
a taron bajekolin na bana da ya gudana a Cibiyar Aliko Dangote Skills & Acquisition Centre.MATASA
Daga cikin matasan masu fikira da suka halarci taron na bana, akwai Khalifa Aminu, matashin da ya ƙirƙiro gilashi da yake taimaka wa makafi wajen yi musu jagora
wanda ya ce a yanzu haka ya sake ƙirƙirar na’urar da ta ke sarrafa kan ta wajen fesa ruwa a gona.
Kazalika, akwai Haruna Badamasi, matashin da ya ƙirƙiro jirgi mara matuƙi, wanda a cewar sa yana taimaka wa manoma wajen feshin magani,
har wa yau jirgin yana da tanki wanda yake iya ɗaukar lita biyu na ruwan maganin ƙwari domin feshin gona.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda ya samu rakiyar Ministan Matasa na Najeriya, Sunday Akin Dare,
ya ce gwamnati za ta ci gaba da tallafawa cibiyar da sauran makarantu masu koyar da ƙere-ƙere mallakin jihar, domin daƙile rashin aikin yi a tsakanin matasa.

