Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Gwamnatin Kano Ta Samar wa Matasa Dubu 10 Da Ayyukan Yi

Gwamnatin Jihar Kano

Gwamnatin Jihar Kano

Gwamnatin Jihar Kano tare da hadin gwiwar gwamnatin tarayya da kuma bankin Duniya sun fara aiwatar da wani shiri na karfafawa matasa dubu 10 wadanda suka hada mata da mutane masu bukatu na musamman a Jihar.

Karanta Wannan: Tsaro: Hukumar Tsaro Ta Civil Deffence Ta Fara Daukar Sabbin Ma’aikata

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, ya bayar da rahoton cewa, shirin karfafan matasan za a yi shi ne ta akarkashin ofishin aikin noma na Najeriya.

Shugaban shirin a Jihar ta Kano, Hassan Ibrahim, ne ya bayyana hakan a lokacin wani taron wayar da kai tare da masu ruwa da tsaki daga kananan  hukumomin Kiru da Bebeji da kuma Madobi, na Jihar.

Shugaban wanda jami’ar sadarwa ta hukumar Rabi Mustapha, ta wakilce shi, ya bayyana cewa wadanda suka ci gajiyar shirin za a koyar da su sana’o’i ne daban-daban domin a karfafi wadanda za su ci gajiyarsa ne a kan sana’o’i mabambanta ta yanda za su zama masu dogaro da kansu.

Ibrahim ya ce, duk wadanda aka zabo bayan an koyar da su za kuma a basu jari kyauta da za su kafa kansu, zuwa yanzun an sami mutane dubu 41 da suka bayyana sha’awarsu daga kananan hukumomi 44 na Jihar, za;a fara tantance takardun su domin tabbatar da cancantar su.

Ya ce ana sa ran kashi 35 na wadanda za su ci gajiyar shirin su kasance mata ne, sannan kuma  kashi biyar kasance Nakasassu ne.

Exit mobile version