Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Tsarin Zaɓe: Za A Yi Muhimman Sauye-Sauye Shida A Najeriya

inec logo big e1548855552200

inec logo big e1548855552200

Hukumar zaɓe ta Najeriya, INEC ta ce ta yi nazari tare da samar da wasu shawarwari kan yadda za a yi wa harkar zaɓe garanbawul domin inganta shi kafin ƙarshen shekarar 2025.

Hukumar ta ce buƙatar yin gyaran ta taso ne daga shawarwarin da ta samu daga masu ruwa da tsaki da suka yi nazari game da yadda aka gudanar da babban zaɓen 2023.

INEC ta ce daga ckin shawarwarin da ta tattara akwai waɗanda ke buƙatar ɗaukar matakin gyara daga ita kanta hukumar da waɗanda suka shafi sauran masu ruwa da tsaki irin su jami’an tsaro da kamfanonin sadarwa da jam’iyyun siyasa da kuma hukumomin tabbatar da ingancin aiki.

Sauran ɓangarorin da buƙatar gyaran ta shafa sun haɗa da ƙungiyoyin masu aikin sufuri da ƙungiyoyin fararen hula da kuma kafafen yaɗa labarai.

Saboda da haka hukumar ta ce za ta gabatar da wani cikakken rahoto mai neman tabbatar da wannan ƙudiri na yin garamabawul ga tsarin zaɓen Najeriya, ga kwamitocin majalisar dokokin tarayya domin su yi aiki a kai da kuma tabbatar da su.

Exit mobile version