Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Hukumar INEC Za Ta Kirkiro Rumfunan Zabe Tare Da Gyaran Mazabu

Hukumar Zabe Mai Zaman Kan Ta kasa, INEC

Hukumar Zabe Mai Zaman Kan Ta kasa, INEC

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC, ta ce a cikin watanni hudun farko na shekara ta 2020, za ta kara kirkiro wasu rumfunan zabe tare da yi wa mazabu gyara a fadin Nijeriya.

Kwamishinan Zabe na Tarayya kuma Jami’in Wayar da Kan Jama’a Festus Okoye ya bayyana haka, yayin da ya ke jawabi a wajen wani taro da hukumar ta yi da Kungiyoyin Rajin Kare Dimokradiyya da Sa-ido kan Zabe a Abuja.

Okoye, ya ce hukumar zabe za ta tuntubi dukkan bangarorin da ke da ruwa da tsaki domin jin ta bakin su game da karin rumfunan zaben da za a yi, ya na mai cewa akwai rumfunan zabe dubu 119 da 973 da kuma wuraren zabe dubu 57 da 73 a fadin Nijeriya.

Ya ce hukumar za ta hada kai da Majalisar Dattawa da ofishin Atoni Janar na Nijeriya domin samun maslahar yadda za a tsara karin da kuma gyaran su ta yadda za su shiga cikin doka.

Exit mobile version