Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Tsara Mulki: Shugaba Bola Ahmed Tinubu Ya Gana Da Gwamnonin APC A Abuja

Shugaban kasa Alhaji Bola Ahmed Tinubu ya yi wani taro da gwamnonin jam’iyyar sa ta APC a fadar sa da ke Abuja, a yau Juma’a.

Gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma, wanda aka zaba kwanan nan a matsayin shugaban kungiyar gwamnonin na APC, ya jagoranci tawagar.

Ganawar dai ta shafi batun nadin ministoci da kuma maganar janye tallafin mai, lamarin da ya tayar da hankalin ‘yan Najeriya a halin yanzu.

Wadanda suka halarci taron sun hada da gwamna Babajide Sanwo-Olu na Lagos, da Abdullahi Sule na Nasarawa, da Umar Namadi na Jigawa, da Inuwa Yahaya na Gombe, da Yahaya Bello na Kogi, da Farfesa Babagana Zulum na Borno, da Mai Mala Buni na Yobe.

Sauran su ne Uba Sani na Kaduna, da Dikko Radda na Katsina, da Hyacinth Alia na Benue, da AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara, da Dapo Abiodun na Ogun, da Umar Bago na Niger, da Aliyu Ahmed na Sokoto, da Francis Nwifuru na Ebonyi da kuma Bassey Otu na Cross River.

Exit mobile version