Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Taron Tinubu Da Gwamnonin APC: Shugaban Kasa Ya Sha Alwashin Inganta Rayuwar Al’Umma

Shugaban kasa Alhaji Bola Ahmed Tinubu, ya ce inganta rayuwar ‘yan Najeriya ne babban abin da gwamnatin sa ta fi ba muhimmanci.

A cewar Daraktan yada labarai na fadar shugaban kasa, Abiodun Oladunjoye, shugaban kasa ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC karkashin jagorancin gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, a fadar gwamnati dake nan Abuja.

Shugaba Tinubu, ya ce gwamnatin tarayya da gwamnonin jihohi za su yi aiki tare a kan mafi karancin albashi, wanda abu ne da ya ce ya kamata a duba.

Shugaban kasa ya bukaci gwamnonin su yi amfani da damar da miliyoyin ‘yan kasa suka ba su domin kawo sauyi a rayuwar jama’a, ya kuma kara da cewa zai yi aiki domin jin dadin ‘yan Najeriya.

Exit mobile version