Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

PDP Ta Yi Barazanar Hukunta Gwamnonin G-5 Kan Hada Kai Da Tinubu

Fusatattun gwamnonin jam’iyyar PDP biyar, sun gana da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu a birnin Landan na kasar Birtaniya.

Fusatattun gwamnonin jam’iyyar PDP biyar, sun gana da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu a birnin Landan na kasar Birtaniya.

Rahotanni sun ce, Tinubu ya nemi amincewar gwamnonin biyar su mara ma shi  baya yayin wani taro da su ka gudanar.

Gwamnonin dai, tare da da wasu jiga-jigan siyasa daga yankin Kudu sun sha alwashin ba za su goyi bayan Atiku Abubakar ba, saboda kin amincewa da shugaban jam’iyyar na kasa Iyorchia Ayu ya yi murabus bayan Atiku ya samu tikitin takara.

Sai dai jam’iyyar PDP ta ce ba ta da masaniya a kan tattaunawar da gwamnonin su ka yi da Tinubu, inda ta ce ta san dai sun tafi hutu kasar Birtaniya.

Jam’iyyar PDP, ta yi barazanar hukunta gwamnonin a kan duk wani aiki da zai saba wa dokokin ta, ta na mai jaddada cewa ta na da karfin ikon ladabtar da duk gwamnan da ya bijire wa dokokin ta.

Exit mobile version