Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Ta’addanci: Kungiyar ISWAP Ta Kama Wasu Ma’aikatan Gwamnatin Barno

Rahotanni daga Jihar Barno sun ce mayakan kungiyar ISWAP sun kama wasu ma’aikatan gwamnatin jihar guda 5 dake kula aikin hanyar garin Chibok zuwa Dambuwa.


Bayanai sun lamarin ya faru ne a ranar larabar da ta gabata a lokacin da mayakan suka afkawa ma’aikatan a kusa da kauyen Wovi dake karamar hukumar Chibok.


Ya zuwa yanzu dai hukumomin Najeriya basu ce komai ba akan lamarin ba.
To sai dai wata majiya ta shaidawa Jaridar Daily Trust cewar ma’aikaci guda da direban motar su sun gudu daga hannun wadanda suka kama su.

Exit mobile version