Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Mayakan ISWAP Sun Kashe Tarin Sojojin Najeriya A Wani Farmaki

Rundunar Sojin Nijeriya, ta tabbatar da mutuwar tarin dakarun ta yayin wani hari da ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram su ka kai masu a yankin tafkin Chadi.

Majiyoyi sun ce, mayakan ISWAP ne su ka kai wa ayarin sojojin Nijeriya hari a kauyen Metele na jihar Borno, lamarin da ya kai ga ba-ta-kashi, inda daya daga cikin ‘yan ta’addan ya tada Bom din da ke daure a jikin sa.

Majiyoyin sojin Nijeriya sun ce an yi asarar dakarun soji da dama, amma ba za su iya fadin adadin wadanda lamarin ya shafa ba.

Rahotanni sun ce, ayarin sojojin su na kan hanyar su ta zuwa garin Arege da ke kan iyakar Nijeriya da Nijar da Chadi, domin kai wa dakarun da su ke yaki da ‘yan ta’adda a yankin abinci ne su ka gamu da harin.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafin ta na yanar gizo, kungiyar ISWAP ta ce lallai ita ta kai harin, kuma bom din da ya tarwatse ya lalata wasu motocin soji masu sulke guda biyu.

Exit mobile version