Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Shettima Da Matar Shugaban Kasa Tinubu Sun Halarci Zaman Majalisar Dattawa

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, da uwargidan
shugaban ƙasa Remi Tinubu, sun halarci zaman bankwana na
majalisar dattawa ta 9.

Majalisar dattawa dai ta yi zaman bankwana a zauren ta da ke birnin tarayya Abuja.

Yayin da ya ke jawabi, mataimakin shugaban kasa ya ƙarfafa zababbun Sanatocin majalisar dattawa ta 10 mai zuwa su sa kishin ƙasa gaba da komai.

A nata bangaren, uwargidan shugaban kasa ta jaddada kalaman Shettima, inda ta tuna wa zaɓaɓɓun ‘yan majalisar su sa kudirin gina kasa a zuƙatan su fiye da burin ƙashin kan su.

Ta ce gwamnatin mai gidan ta ta na buƙatar gogewa da kwarewar ‘yan majalisa masu barin gado nan da ranar 13 ga watan Yuni.

Exit mobile version