Dakarun soji da ke yakar ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram da ISWAP guda 80, a yayin da wasu 876 suka mika wuya a makonni biyun da suka gabata.
Mai Magana da yawun rundunar, Manjo-Janar Musa Danmadami, ya ce sojojin hadin gwiwa da ke Tafkin Chadi MNJTF sun kashe kwamandoji da mayakan kungiyar ISWAP 55 a yankin Arege da ke Karamar Hukumar Abadam ta Jihar Borno.
Ya ce sojojin sun kuma kashe mayakan Boko Haram da ISWAP 25, suka kwato bindigogi 30 da sundukan albarusan AK-47 guda 12 da gurneti daya da sauran makamai.
Manjo-Janar Danmadami ya kara da cewa an kashe kwamandojin kungiyar da dama a wani samame na kwana 22 wanda ya kare a ranar 28 ga Mayu, 2023 a yankin Harbin Zuma da ke Gabar Tafkin Chadi.

