Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Sa’in Katsina Alhaji Ahmadu Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

images (51)

images (51)

Mun samu labarin rasuwar Sa’in Kastina Alhaji Amadu da ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara sama da 90.

Alhaji Amadu ya rasu ne a ranar Alhamis a Asibitin Koyarwa ta Tarayya da ke Katsina bayan ya yi fama da rashin lafiya.

Marigayin shi ne Sa’in Katsina na farko kuma shi ne dan majalisar Sarki da ya fi kowa dadewa.

Sa’in Katsina ya yi zamani da sarakunan Katsina uku, Sa Usman Nagogo, Sarki Kabir Usman Nagogo da kuma Sarki na yanzu Abdulmuminu Kabir.

Marigayin dan uwa ne ga tsohon Sojan nan Abba Siri-siri kuma ya yi tashe a harkokin siyasa tun a zaman da ya yi a kasar Saliyo kafin dawowar sa gida Najeriya.

Marigayi sa’ain Katsina Alhaji Ahmadu Na Funtuwa, Mutun ne mai son ganin ba a yi watsi da harkokin addini da na al’adu ba tare da wasannin motsa jiki.

Daga cikin ’ya’yan da ya bari akwai Alhaji Muntari Sa’i da sauran su gami da jikoki masu yawa.

Exit mobile version