Mukaddashin Akanta-Janar na tarayya Anamekwe Nwabuoku, ya ce halin da Nijeriya ke ciki a yanzu sai an ciwo bashi kafin a iya biyan albashin ma’aikatan gwamnati.
Anamekwe Nwabuoku ya bayyana haka ne, a wani taro da aka shirya wa ‘yan kwamitin tattalin kudi a Abuja, inda ya ce adadin kudin da gwamnati ke kashewa yanzu ya yi tashin gwauron zabo sakamakon matsalar tsaro da bukatar taimaka wa al’umma, don haka sai sun karbi bashi kafin su iya biyan albashin ma’aikata.
Babban Akantan ya cigaba da cewa, lissafin su ya nuna cewa sakamakon rashin kudin shiga, baitul-malin gwamnati ya koma neman rance domin biyan albashin ma’aikatan tarayya.
Anamekwe ya bada shawarar yadda za a shawo kan lamarin ta hanyar tattalin kudi, da fadada hanyoyin samun kudi da toshe hanyoyin sata da fitar da kayayyki waje.

