Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Karin Albashi: Gwamnati Na Nazarin Iya Aiwatar Da Sabon Tsarin

Wasu rahotanni na cewa, har yanzu akwai sauran aiki kafin gwamnatin Nijeriya ta shawo kan iya biyan sabon tsarin albashin ma’aikata.

Idan dai za a iya tunawa, tuni shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan dokar da ta ce kowane ma’aikaci zai rika samun akalla Naira 30, 000 a matsayin albashi duk wata.

Sai dai bincike ya nuna cewa, biyan sabon albashi ba zai zo wa gwamnati da sauki ba, domin tsarin tattalin arzikin Nijeriya na cikin gida ya na da rauni.

Wata majiya ta ce, rashin isassun kudin-shiga zai sa Nijeriya ta duba yiwuwar kara harajin kayayyaki, domin a iya biyan kowane Ma’aikaci abin da bai gaza Naira 30, 000 ba.

Wata hanya kuma da gwamnati ta ke dubawa domin samun kudin da za a rika biyan albashi ita ce tallafin man fetur, wanda Gwamnatin tarayya na iya daina biyan shi don ta iya biyan albashin.

Exit mobile version