Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Sai Kun Zama Masu Bin Doka Za Ku Iya Kama Masu Karya Doka, Kiran IGP Ga ‘Yan Sanda

Muƙaddashin shugaban ‘Yan Sandan Nijeriya Olukayode
Egbetokun, ya umarci tawagar motocin ‘yan sanda su daina
saɓa dokokin amfani da hanya.

IGP Olukayode ya bada umarnin ne, yayin ganawa da tawagar ‘yan sandan kwantar da tarzoma da kwamndojin ‘yan sanda a Babban Ofishin Rundunar ‘Yan Sanda da ke Abuja.

Egbetokun, ya jaddada wa jami’an su sani cewa, tabbatar da bin doka da oda da kare rayuka da dukiyoyin jama’a shi ne babban aikin su.

Ya ce wajibi ne ‘yan sanda su yi aiki daidai da dokokin aikin ɗan sanda, kuma a cikin yanayin da zai sa al’umma su martaba su.

Exit mobile version