Rundunar ‘yansandan jihar Zamfara ta kama wani dan kasar Aljeriya mai shekara 58 bisa zargin safarar makamai ta kan iyaka.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Mohammed Dalijan ne ya bayyana haka a Gusau ranar Talata.
Ya ce, ‘yansandan sun kwato bindiga kirar AK-47 guda 16, a samame daban-daban a cikin mako uku da suka gabata.