Gwamnatin tarayya ta ce hukumar lafiya ta duniya WHO za ta gwada maganin cutar Coronavirus a kan mutane a birnin Abuja da jihohin Legas da Ogun da Kaduna da Sokoto da Kano.
Gwajin maganin wani kakarin da hukumar ta ke yi domin samar da magani da kuma riga-kafin COVID-19 a cikin kankanin lokaci.
Ministan lafiya Osagie Ehanire ya sanar da haka a lokacin da ya ke jawabi a kan inda kwamitin yaki da cutar Coronavirus da shugaban kasa Buhari ya kwana a aikin sa.
Haka kuma, ministan ya ce a ranar Lahadin da ta gabata, Nijeriya ta kara gwajin samfurin mutane dubu 1 da 127, wanda hakan ya bada jimillar gwajin mutane dubu 27 da 078, dubu 4 da 399 daga cikin su suna dauke da cutar COVID-19 a jihohi 35 na Nijeriya.
Osagie Ehanire ya kara da cewa, gwamnatin tarayya na ba hukumar lafiya ta duniya WHO hadin kai domin gwajin maganin cutar korona a jihohin Legas da Abuja da Ogun da Kaduna da Sokoto da kuma Kano, a wani mataki na kawo karshen yaduwar cutar a fadin Nijeriya.