Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya danganta hauhawar miyagun ayyukan ‘yan bindiga da ‘yan ta’addan Boko Haram da ‘yan siyasa masu son takara a 2023.
Wannan na zuwa ne bayan da ‘yan bindiga a jihar Zamfara suka mika bindigogi 50 a makon da ya gabata, domin amincewa da karbar shanu biyu da gwamnan ya ce zai bada ga duk wanda ya kawo bindiga daya.
Gwamnan ya ce, wadannan ‘yan siyasar sun yadda cewa ta hanyar daukar nauyin ‘yan bindiga da sauran ‘yan ta’adda ne kawai za su iya bata wa mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari suna don samun damar mulki.
Masari, wanda ya yi wannan jawabin tare da shugabannin gunduma da kananan hukumomi na APC, ya ce da yawa daga cikin ‘yan bindigar da ‘yan Boko Haram da ke kai hari bin umarnin wasu ‘yan siyasa ne.