Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Ta’addanci: Tubabbun ‘Yan Bindiga A Jihar Katsina Sun Fasa Kwai

Tubabbun ‘yan bindiga a jihar Katsina, sun sanar da gwamnan jihar Aminu Bello Masari cewa, wasu daga cikin jami’an ‘yan sanda da soji ne ke rura wutar ayyukan ta’addanci a jihar domin su samu kudi.

‘Yan bindigar sun yi gargadin cewa, matukar jami’an tsaro ba su daina karbar kudi da shanu daga hannun su ba, ba za a samu wani sauyi ta fuskar samun zaman lafiya a jihar ba.

Kungiyoyin ‘yan bindigar sun bayyana haka ne, yayin wata tattunawa da gwamna Masari a wani zaman sulhu da aka fara yi a makarantar Firamare ta Gbagegi da ke Dankolo a yankin karamar hukumar Dandume.

Tubabbun ‘yan bindigar da su ka gana da gwamnan, sun fito ne daga kananan hukumomin Dandume da Sabuwa, kananan hukumomin da hare-haren ‘yan bindigar su ka fi tsananta.

Yawaitar hare-haren ‘yan bindiga da satar shanu da garkuwa da mutane ne su ka tilasta Masari yanke shawarar yin sulhu da ‘yan ta’addar domin samun zaman lafiya, sai dai shugaban kungiyar ‘yan bindigar Idris Yayande, ya fada wa Masari cewa hallayyar jami’an tsaro ta karbar kudi daga hannu su ya sa duk kokarin gwamnatin sa na tabbatar da zaman lafiya ya ki yin wani tasiri.

Exit mobile version