Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Ministan Shari’a Ya Bukaci A Rushe Hukumar Zaben Jihohi

FAGBEMI 1200x729

FAGBEMI 1200x729

Babban lauyan gwamnatin tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, ya bukaci a soke hukumomin zabe na Jihohi wato SIECOM.

Ministan ya ce, mayar da ayyukan su ga hukumar zabe ta kasa wato INEC zai tabbatar da ’yanci na gaskiya da samar da sakamakon zaben mai inganci.


Lateef Fagbemi ya bayyana wa taron kasa kan kalubalen tsaro da shugabanci na gari a Najeriya a matakin kananan hukumomi,


ta shirya cewa, soke kwamishinonin jihohi zai yi tasiri gami da ba da dama dimokaradiyya ta samu gindin zama a kananan hukumomi.


Hakan a cewar sa, zai kawar da duk matsalolin da ke kawo cikas ga ci gaban kananan hukumomi da kuma iya gudanar da ayyukan su da tsarin mulki ya amince da su.


Ya ce duk da tanade-tanaden da tsarin mulki ya yi na tabbatar da ’yancin hukumomi, gwamnatocin jahohin na ci gaba ruguza su ba bisa ka’ida ba,


Ya kara da cewa, asusun bai-ɗaya na jihohi da kananan hukumomi ne ya hana kananan hukumomin ci gaba tun fara jamhuriya ta hudu.

Exit mobile version