Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

ZA A GUDANAR DA ZABUKAN CIKE GURBI NA GWAMNONI DA NA ‘YAN MAJALISU A NAJERIYA

A ranar Asabar 15 ga watan Afrilun nan ne, ake sa ran
hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa za ta gudanar da
zabubbukan cike gurbi, domin tantance wadanda su ka samu
nasara a zaben gwamnonin Jihohin Adamawa da Kebbi da
kuma majalisun tarayya a yankunan da ba’a kammala ba.

A wata sanarwa da hukumar zabe ta fitar, ta ce za a gudanar da zabubbukan ne a rumfunan zabe da mazabu dubu 2 da 660, a kananan hukumomi 185 da ke jihohi 24, inda za a yi zaben gwamna a mazabu 69 da ke kananan hukumomi 20 na jihar Adamawa, yayin da a jihar Kebbi za a yi zaben ne a mazabu 142.

A bangaren majalisar dattawa kuwa, za a gudanar da zaben cike gurbin ne a jihohin Sokoto da Kebbi da kuma Zamfara, domin tantance wadanda su ka samu nasara daga zaben da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu wanda bai kammala ba.

Hukumar zaben ta ce za a gudanar da zabe a mazabu 389 da ke kananan hukumomi 23 a jihar Sokoto, domin tabbatar da wadanda su ka samu nasarar zuwa majalisun dattawa guda 3 da ke jihar, yayin da a jihar Zamfara za a gudanar da zabe ne a mazabu 83 da ke mazabar Zamfara ta tsakiya.

Exit mobile version