Kungiyar Malaman makarantun kimiyya da fasaha na Nijeriya ASUP, ta sanar da cewa ta yanke shawarar shiga yajin aikin garga]i na makonni biyu daga ranar 16 ga watan Mayu na shekara ta 2022.
Wata kwakkwarar majiya ta ce, kungiyar ASUP ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar.
Sanarwar ta ce, Malaman makarantun sun yanke shawarar shiga yajin ne, bayan zaman majalisar zartarwa
ta kungiyar da aka yi a ranar Larabar nan.

