Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Ma Ba Neman Matawalle Ruwa A Jallo – EFCC

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC, ta karyata zargin cewa ta na neman tsohon gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ruwa a jallo.

A Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafin ta na Twitter, EFCC ta ce ta fitar da sanarwar ne bayan jan hankalin ta da aka yi a kan rahoton wata jarida, wadda ta wallafa cewa ta na neman Matawalle ruwa a jallo.

EFCC ta ce rahoton ba daidai ba ne, domin ya zuwa yanzu ba ta ayyana Matawalle a matsayin wanda ta ke nema ko neman hukumar DSS ta kama mata shi ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa, EFCC ta na da tsarin da ta ke bi wajen ayyana mutum a matsayin wanda ta ke nema, kuma ta na da hanyoyin da ta ke bi ta sanar da mutane ta na neman shi ba ta hanyar amfani da majiyoyin bogi ba.

Exit mobile version