Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Kungiyar ASUU Ta Bukaci Soke Jarrabawar Jami’ar Jihar Kaduna

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya ASUU, ta yi kira ga mahukuntan Jami’ar Jihar Kaduna KASU, su soke jarrabawar da ake yi a makarantar har sai an dakatar da yajin aikin da kungiyar ke yi a fadin kasar nan.

ASUU ta ce dole ne a sake gudanar da jarrabawar lokacin da kungiyar ta janye yajin aikin ta.

Hukumar gudanarwa ta Jami’ar Jihar Kaduna dai ta sake bude jami’ar, yayin da reshen ASUU na Jami’ar ya bijire wa Barazanar Gwamnan El-Rufa’i, inda Malaman su ka tsaya kai da Kafa cewa har yanzu yajin aikin na ci-gaba da gudana.

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in kungiyar ASUU na shiyyar Kano Kwamared Abdulkadir Muhammad, ya ce idan har mahukuntan jami’ar su ka ki soke jarabawar, kungiyar za ta kasance ba ta da wani zabi illa rubuta takardar koke ga hukumar jami’o’i ta kasa NUC da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ICPC.

Exit mobile version