Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Kuncin Rayuwa: ACF Ta Dora Laifi Kan Manufofin Gwamnatin

ACF (2)

ACF (2)

ACF ta koka kan yadda wasu manufofin gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ke haddasa taɓarɓarewar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki da kuma rashin aikin yi.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne bayan taron majalisar zartarwar ta ta ƙasa da ya gudanar a Kaduna a jiya Talata.

Kungiyar ta ACF ta kuma yi gargaɗin cewa Najeriya na iya fuskantar ruɗanin zamantakewa, musamman a yankin Arewa idan ba a yi wani abu domin magance taɓarɓarewar tattalin arziki ba.

Ta ce ta lura cewa ana a ci gaba da rayuwa cikin wahala da ƙalubale, inda kullum talakawan Najeriya ke fuskantar matsalar hauhawar farashin kayayyaki da rashin aikin yi,

da saurin taɓarɓarewar rayuwa tare da tashe-tashen hankula, da aikata ta’addanci da kuma barazanar ‘yan bindiga.

A cikin sanarwar da kakakin ƙungiyar na ƙasa Farfesa Tukur Muhammad-Baba ya fitar kuma ya sanya wa hannu,

ya koka da yadda matsalolin suka ci gaba da taɓarɓarewa a wasu wurare musamman a Arewa.

Ya ɗora alhakin taɓarɓarewar tattalin arziki a kan cire tallafin man fetur, da kuma haraji da gwamnatin tarayya ta yi,

yana mai cewa waɗannan manufofin ne ke haifar da raguwar walwalar yanayin rayuwar ’yan ƙasa.

Exit mobile version