Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Kotun Ƙoli Ta Yi Watsi Da Umarnin Buhari Na Ba Majalisun Jihohi ‘Yancin Kai

Kotun Ƙoli ta ayyana umarnin gwamnati da Shugaba Muhammadu Buhari ya bada na ba kotuna da majalisun jihohi ‘yancin cin gashin kan su a matsayin wadda ta saɓa wa kundin tsarin mulki.

Shugaba Buhari dai ya sanya wa dokar mai laƙabin Lamba 10 hannu a ranar 22 ga watan Mayu na shekara ta 2020, da zummar ba ɓangaren shari’a da majalisun dokoki na jihohi ‘yancin cin gashin kan su ba tare da sa hannun gwamnatin jiha ba.

Sai dai shida daga cikin bakwai na alƙalan kotun sun amince da cewa, shugaba Buhari ya wuce ƙarfin ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi wajen bada umarnin, don haka su ka ce ta saɓa wa doka.

A wata shari’a ta daban kuma, kotun koli ta kori ƙarar da gwamnoni su ka shigar a kan gwamnatin tarayya, inda su ka nemi ta biya su naira biliyan 66 da su ka kashe wajen tafiyar da kotunan da kuma manyan ayyuka.

Exit mobile version