Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Kotu Ta Dage Sauraron Shari’a, Ta Saka Sabuwa Ranar Zama

Kotun masana’antu ta dage sauararrn shari’ar gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i ta Nijeriya ASUU, zuwa ranar 16 ga watan Satumba na shekara ta 2022.

Mai shari’a Polycarp Hamman ya dage sauraren shari’ar ne, domin a ba gwamnatin tarayya damar mika dukkan takardun da su ka dace a kan karar.

Gwamnatin tarayya dai ta garzaya gaban kotun masa’antu ta kasa da ke Abuja, inda ta bukaci a umarci kungiyar malaman jami’o’i su koma bakin aiki, yayin da ake kokarin shawo kan rashin jituwar da ke tsakanin su.

A wata takarda da jami’in yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar kwadago Olajide Oshundun ya fitar, ya ce a ranar 8 ga watan Satumba ne ministan kwadago ya aike da lamarin gaban maga-takardan kotun masana’antu.

Kungiyar ASUU dai ta shiga yajin aikin makonni hudu a ranar 14 ga watan Fabrairu, sannan ta cigaba duk da tattaunawar da ta ke yi da gwamnatin tarayya ba a samu matsaya ba.

Exit mobile version