Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Gwamnati Ta Yi Daidai Da Ta Hana Asuu Albashi – Kotu

Kotun kwadago ta Nijeriya, ta zartar da hukuncin cewa
matakin da gwamnatin tarayya ta dauka a kan kungiyar
Malaman Jami’o’i na kin biyan ma’aikatan da su ka shiga
yajin aiki albashi ya na kan doka.

Shugaban kotun mai shari’a Benedict Kanyip ya bayyana haka yayin da ya ke sanar da hukuncin, inda ya ce gwamnatin tarayya ta na da ikon rike albashin ma’aikatan da su ka shiga yajin aiki.

Sai dai a bangaren tsarin biyan albashi, kotun ta zartar da cewa, ya saba wa tsarin ‘yancin cin gashin kai na jami’a a tilasta wa malaman shiga tsarin biyan labashi na IPPIS, saboda malaman su na da ‘yancin zaben yadda za a biya su albashin su.

A ranar 14 ga watan Fabarairu ne kungiyar ASUU ta shiga yajin aiki na tsawon watanni takwas, a kan neman kyautata yanayin albashi da inganta tsarin ilimin jami’a da sauran bukatu.

Exit mobile version