Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Ko Ana So Ko Ba A So Sai Na Zama Shugaban Kasa A Nijeriya – Peter Obi

Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Peter Obi, ya
jaddada cewa ko tantam ba ya yi sai ya mulki ‘yan Nijeriya.

Da ya ke jawabi a wajen kaddamar da wani littafi a birnin Awka na jihar Anambra, Peter Obi ya ce masu tunanin ba zai zama shugaban Nijeriya ruɗin kan su su ke yi, domin sai ya shiga fadar shugaban kasa kuma ya mulki ‘yan Nijeriya.

Ya ce ma su ganin ba zai zama shugaban kasa ba su sani cewa mafarki su ke yi, amma mulkin Nijeriya kamar ya yi ya gama ne, ya na mai cewa dole ya zama shugaban Nijeriya ko ana so ko ba a so.

Peter Obi ya cigaba da cewa, ba ya da takardar zama ɗan wata kasa ban da Nijeriya kuma babu inda zai je.

Exit mobile version