Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Gwamnatin Tarayya Ta Musanta Belin Peter Obi Daga Hannun Birtaniya

Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour, ya ce jami’ai sun tsare, tare da hantarar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Peter Obi a birnin London.

Gwamnatin Tarayya, ta musunta labarin da ke cewa ta shiga
tsakani a kan tsare dan takarar shugaban kasa na jami’yyar
Labour Peter Obi da aka yi a Birtaniya.

Idan dai ba a manta ba, an tsare Peter Obi na dan wani lokaci a filin jirgin saman Hearthrow da ke London, bisa rashin gane ko shi wanene bayan ya je kasar domin gudanar da bikin Easter.

A ranar Alhamis da ta gabata ne, wani hoton bogi ya karade kafafen sada zumunta, inda ya nuna shugabar hukumar ‘yan Nijeriya mazauna kasar waje Abike Dabiri-Erewa zaune a wani ofis tare da Peter Obi da wani jami’in tsaron Birtaniya domin neman karbar belin sa.

Sai dai mai shugaban sashen yada labarai kuma kakakin hukumar Abdur-Rahman Balogun ya musunta labarin, inda ya ce Dabiri-Erewa ba ta je Birtaniya ba, kuma ba ta da hurumin
neman belin kowane dan Nijeriya da ake zargi da aikata laifi a Birtaniya.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafin sa na Twitter, mai taimaka wa shugaban kasa a kan shafukan sada zumunta Bashir Ahmad, ya nesanta gwamnatin tarayya da neman belin Peter Obi bayan tsare shin da jami’an tsaro su ka yi a Birtaniya.

Exit mobile version