Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Karancin Ruwa A Kano: Abba Gida-Gida Ya Ayyana Dokar Ta Baci

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya ayyana dokar ta baci a kan matsalar karancin ruwan famfo a jihar, inda ya bada wa’adin mako guda Hukumar Ruwa ta Jihar Kano ta mika bukatun su tare da kawo karshen matsalar karancin ruwa da ake fama da shi.

Abba Kabir Yusuf  ya bayyana haka ne, lokacin da ya ziyarci cibiyar kula da ruwa ta Challawa, inda ya ce wannan ya na daga cikin matakan da gwamnatin shi ta maida hankali wajen dakile matsalar karancin ruwa a fadin jihar Kano.

A yayin ziyarar, gwamnan ya nuna rashin jin dadin sa a kan yanayin da ya samu kayan aiki a cibiyar kula da ruwan, inda ya ce nan ba da jimawa ba batun karancin ruwan zai zama tarihi a Jihar Kano.

Ya ce gwamnatin jihar za ta cika alkawurran da ta dauka a lokacin yakin neman zabe, don haka ya bukaci mazauna Kano su ba shi hadin kai.

Exit mobile version