Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Ban Yi Nadamar Rusau A Kano Ba – Abba Gida-Gida

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya ce bai yi da-na-
sanin rushe-rushen da ya gudanar da kuma kwace kadarorin
al’umma da aka mallaka ba bisa ka’ida a jihar ba.

Abba Kabir ya bayyana haka ne, lokacin da ya karbi bakuncin Sarkin Kano Alhaji Aminu Bayero da wasu hakimai, yayin da su ka kai ma shi gaisuwar Sallah a gidan gwamnatin jihar.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Hisham Habib ya fitar, ta ce ya na da kyau ga masarautar Kano ta san da cewa sun kudiri aniyar rusau ne domin dawo da kadarorin al’umma da aka mallaka ba bisa ka’ida ba, kuma za su tabbatar duk irin wadannan kadarorin sun dawo da su saboda al’ummar Jihar Kano.

Tun farko Sarkin Kano ya ce ya kai wa gwamnan ziyara ne domin yi masa gaisuwar Sallah, da kuma tabbatar ma shi cewa a shirye ya ke ya ba shi shawarwarin da za su kawo ci- gaba ga jihar Kano.

Sarkin Kano, ya kuma bukaci gwamnatin Kano ta fito da sabbin tsare-tsare domin taimaka wa al’ummar jihar domin rage masu radadin cire tallafin man fetur.

Exit mobile version