Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Karamar Hukumar Sabon Birni Ta Zama Tarkon Mutuwa

Gunmen kill health worker abduct two wives four children in Jangebe

Gunmen kill health worker abduct two wives four children in Jangebe

Rahotanni daga jihar Sokoto a arewa maso yammacin Najeriya, na cewa ‘yan bindiga a yankin Sabon Birni na ci gaba da satar jama’a masu dimbin yawa tare da kashe wasu.

Bayanan sun ce ‘yan fashin dajin na ci gaba da rike akalla mutum 150 baya ga karin wasu ashirin da takwas da aka sace a karshen makon nan a kauyen Makuwaana da ke karamar hukumar Sabon Birnin.

Wannan na zuwa ne kasa da mako guda da wasu masu garkuwa da mutane suka kashe Sarkin Gobir na Gatawa, Alhaji Isa Muhammad Bawa.

Lamarin ya faru kwanaki bayan da wasu ‘yan bindiga da suka yi garkuwa da sarkin da dansa da wasu karin mutum shida a hanyarsu ta zuwa birnin Sokoto.

Alummar garin Sun ce Ba bu ranar da ‘yan bindiga ba su shigowa kauyuka, sansanonin da a garesu kewayen kauyukan suna daukar jama’a, ainihin ranar da aka yi sanarwar ba bu ran sarki,

daddaren nan sai da suka shiga kauyen ‘yan Haru mai nisan kilomita biyu da sabon birni inda suka dauki mutum fiye 20 bayan mutum fiye da 10 da suka yi garkuwa da su.

Wani mutum a yankin ya ce mazauna garuruwan Tsammaye da ungwar Lalle su na shirin tashi ya kuma yi ikirrain cewa ba bu wani ‘mataki da mahukuntan suka dauka’.

Exit mobile version