Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Garkuwa Da Mutane: Wasu Kananan Yara Sun Kubuta Bayan Kwana 60 A Hannun ‘Yan Bindiga

Wasu kananan yara ’yan gida daya masu shekara 10 sun kubuta daga hannun masu garkuwa bayan sun kwashe kwana 60 a hannun su.

Yaran sunce su 16 ne suka tsere daga hannun masu garkuwar, ciki har da wata mai jego da wata amarya daga da ’yan tawagarta da aka yi garkuwa da su a hanyarsu ta kai amaryar dakin mijinta a Jihar Kaduna.

Tun a ranar 9 ga watan Yunin 2021 aka sace su akan hanyar sun a zuwa Anguwar Dutsen Abba a Karamar hukumar Zariya dake Jihar.

Da yake nuna godiyarsa ga Allah, mahaifin yaran, yace “A ranar Lahadi 8 ga watan takwas ne aka bugo masa waya daga gidan Dakacin Sabon Birni, cewa ga wasu yara uku daga cikin wadanda suka kubuta daga hannun ‘yan Bindiga.

Kuma “Da ma acewarsa yaran na cikin mutum 11 da aka sace amma an sako wasu daga ciki bayan biyan kudi har miliyan uku da kuma babur daya.

Ya bayyana cewa daga cikin yaran da suka kubuto akwai mace mai shekara 10 da kannenta biyu, sai kuma wata mai shekara bakwai da watanni, da kuma kaninsu mai shekara bakwai.

Yanzu haka dai bayan an kai su asibiti domin duba lafiyarsu, tuni an hada su da ’yan uwan su.

Exit mobile version