Gwamnatin Jihar Zamfara ta umarci dukkanin kungiyoyi masu zaman kansu da ke aiki a jihar su tattara nasu-inasu su fice daga jihar ba tare da bata wani lokaci ba.
Umarnin na cikin wata sanarwa ne da Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Mamman Tsafe ya fitar.
Sanarwar ta zargi kungiyoyin wadanda ba na gwamnati ba da gudanar da ayyukan da ke iya kara matsalar tsaro a jihar da makwabta ganin yadda kungiyoyin suke ta karuwa a jihar inda suke gudanar da ayyukan da suka saba wa doka, har ila yau yawancin kungiyoyin ba su yi rijista a jihar ba kamar yadda doka ta tanada.
Sanarwar ta umarci ma’aikatu da sassa da kuma hukumomin gwamnati su daina duk wata mu’amulla da kowa ce kungiya, tare da gargadin cewa za a hukunta duk wata hukumar gwamnati da ta yi mua’mulla da kungiyoyin.
Gwamnatin ta kuma bayar da umarni ga hukumomin tsaro su sanya ido domin gano duk wata kungiya da ke aiki ba tare da takardar izini daga hukumar da ta dace ba, domin gurfanar da ita a gaban kotu.