Gwamnatin jihar Sokoto ta haramta ayyukan ƴan sa-kai a faɗin jihar tare da ƙarfafa aikin ƴan banga.
Gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal wanda ya sanar da ɗaukar matakin a ranar Litinin a wani taron tsaro na jihar, ya ce sha’anin yan sa-kai shi ya ƙara haifar da matsala a Zamfara da jihohin da ke maƙwabtaka da ita.
Gwamnan ya ce ‘yan sa kan suna yin gaban kan su ne ba tare da bin doka da oda ba, dan haka ba za su ci gaba da kyalewa ba domin sun san illar hakan.
Tambuwal ya ce yanzun sun fito da doka da ta haramta ƴan sa-kai kuma duk wanda ke son taimakawa jami’an tsaro, to ya shiga aikin banga, Sanarwar da ofishin gwamnan ta fitar ta ce duk wanda aka kama zai sha ɗaurin shekara 14 ko biyan tara ta naira dubu 500.
Dokar ta kuma ce duk wanda aka kama da makami a jihar zai sha ɗaurin shekara bakwai a gidan yari ko ya biya tarar naira 200,000.
Gwamna Tambuwal ya ce gwamnatin sa ta ɗauki matakin ne domin magance matsalolin tsaro da ke damun jihar, kuma matakan hanyoyi ne na inganta sha’anin aikin ƴan banga don taimakawa jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya.